
Rundunar sojojin Najeriya sun dakile harin yan kungiyar ISWAP dana Boko Haram a Jakana na jihar Borno a ranar Lahadi da safe.
Yan kungiyar sun shiga yankin da motar yaki mai dauke da bindiga da kuma gurneti.
Wani dan jarida mai kawo bayanan sirri yace rundunar sojojin saman Najeriya sun taimakawa sojojin kasa wajen dakile harin yan ta’addan.
Wata majiya ta nuna cewa yan ta’addan suna so su shiga garin ne domin diban magunguna da kayakin abinci tare da kwashe makaman jami’an sojoji.
Jakana mai nisan kilomita 25 daga Maiduguri, ya kasance hanyar wucewar yan ta’addan ISWAP zuwa sansanin su dake dajin Benisheikh da kuma mabuyar su dake Buni Yadi na jihar Yobe.
Yan ta’addan sun sha kai hari yankin cikin kayan sojoji inda suke kafa shingen kan titi domin garkuwa da matafiya.
