Rundunar Sojoji Najeriya sun Baiyana Adadin Boko Haram Da Suka Kashe Tun Daga Ranan 18 Na Watan Mayu Zuwa 30 Na Watan Decemba

DHQ TROOPS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojojin Najeriya tace ta kasha yan ta’adda dubu biyu da dari hudu da uku a ayyukan tabbatar da tsaro a kasar daga 18 na watan mayu zuwa 30 na watan decemba daya shude inji mai magana da yawun rundunar tsaron kasa Maj.-Gen. John Enenche.

Eneche ya bayyana sakamakon ranar alhamis yayin da’ake gudanar da ba’asin nasarorin da rundunar ta tsaro tayi a kasa.

Ya kara da cewar rundunar tsaron tayi nasara wajen ceto waddanda akayi garkuwa dasu su dari takwas da sittin da hudu.

Lokacin da yake bada bayanin, yace a arewa maso yammacin kasar an samu dabbobi dubu biyar da dari biyu da tamanin da daya, makaman yaki dubu shida da dari tara da hamsin da daya da manyan bindigogi dari da ishirin da suka karba a hannun yan ta’addan.

Ya kara da cewa a kubutar da mutane dari hudu da hamsin da biyar daga hannun yan ta’addan tareda kashe yan ta’adda dari hudu da saba’in da uku a lokacin.

Eneche yace a ayyukansu na arewa maso gabas, dakarun rundunar operation Lafiya Dole sun kubutar da mutane dari biyu day an ta’addar sukayi garkuwa dasu.

A bayanin sa, an karbi makaman yaki dubu daya da dari uku da tamanin da biyar, bama-bamai arba’in da biyar da manyan bindigogi cassa’in da biyar daga hannun yan boko haram da Islamic West Africa Province ISWAP a watanni goma dasuka wuce.

Ya kara da cewa dakarun sunyi nasarar lalata matatar bogi guda tamanin da biyar, tonannun ramuka tamanin da biyar, da kuma tankuna karafa dari da sittin da uku.
Yace an kubutar da mutane arba’in da bakwai wadanda akayi garkuwa dasu a kudu maso kudu tareda kama masu laifin saba’in da biyu.

Ya kammala da mika godiyar sa wajen al’umma kan hadin kan dasu bawa masu kula da harkar ta tsaro ta hanyar basu bayanai da dama.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply