Rundunar Sojoji Da Yan Sanda Sun Ceto Matasa 25 Da Akayi Garkuwa Dasu A Jihar Taraba

troop3
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar hada ka na sojoji da yan sanda a tare sun ceto matasa 25 da akayi garkuwa dasu a hanyar Wukari zuwa Takum na jihar Taraba.

Jami’i mai hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar na rikon kwarya ASP.

Reform Leha, shi ya bayana hakan ga wakilin gidan rediyo Dandal Kura International Ahmed Umar Gosal a jihar Taraba, wanda ya bayyana mana cewa an ceto su cikin koshin lafiya.

Wani ma’aikaci ya shaida ma wakilin namu cewa an dauki sa’o’i da dama yayin ceton cikin wani daji dake iyakar jihar Taraba da Benue.

Daya daga cikin iyalan wadanda aka ceton Alhaji Baba Muhammed, ya bayyana wa yan jaridu cewa tuni ana bikin murna a yankin Anguwan Rogo na karamar hukumar Takum wanda dukkan matasan sun fito ne daga yankin.

Kafin ceto su a ranar jumma’a daya gabata, wadanda sukayi garkuwan dasu sun nemi kudin fansa naira miliyan 52.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply