Rundunar Sojin Sojin Saman Najeriya Sun Ce Daukar Ma’aikata Kyauta Ne

air
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin saman Najeriya ta jaddada cewa daukar ma’aikata data fara kyauta ne kuma ana kudanar dashi a bude bawai a boye ba.

Daraktan yada labarai da hulda da jama’a Ibikunle Daramola ne ya fitar da rahoton a Abuja, inda yace sun samu labarin cewa wasu yan damfara sun bude shafin Facebook da Whatsapp inda suke son karbar kudi daga hannun mutane.
Daramola yace mutane nayiwa masu neman aikin karyar cewa zasu basu aikin a rundunar sojin saman.

Rundunar tace ta jaddadawa sashin daukar aikin cewa daukan aikin na rundunar cewa za’a dauka ba tare da kudi ba.
Ana sa ran wadanda suka cancanta kamar yadda aka wallafa a jaridun Nation da Daily Trust ranar 10 ga watan Yuli na shekarar 2020 zasu cike ta hanyar yanar gizo a shafinsu mai suna www.airforce.mil.ng.

Haka nan rundunar na nan na shirin daukar mataki ga wadanda suka gudanar da wan nan aikin san nan yayi kira ga wadanda aka ce su biya kudadn dasu kai rahoto sashin rundunar ko ofishin yansanda.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply