Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Ja Hankali Kan Rahoton Da Ke Cewa Jirginsu Ya Kashe Jami’an Soji 20 A Garin Mainok

Rundunar sojin saman Najeriya tace anja hankalinta kan rahoton da ake yadawa cewa jirginsu ya kashe jami’an soji 20 ba da saninsa ba sakamaon barin wuta da yayi a garin Mainok dake da nisan kilomita 55 zuwa Maiduguri.

Rundunar tace suna nan suna binciken rahoton da ake yadawar kuma zasu sanar da jama’a idan sun kammala binciken.
Dabal Kura Radio International ta samo wan nan rahoton a shafinsu na twitter a yau da rana.

Acewarsu sun bi duk hanyoyin day a dace kuma duk mai wani tambaya ya tura zuwa ofishin Daraktan hulda da jama’a da bada bayanai na hedikwatars rundunara ta sojin sama ko kuma ya tura sako a shafinsu na yanar gizo kan info@airforce.mil.ng.