jirgin yaki na Sojojin Sama na Najeriya (NAF) a ranar Lahadi ya kawar da yawancin ISWAP-Boko Haram ‘yan ta’adda ciki har da kwamandojinsu a Lamboa dake karamar hukumar Kaga a jihar Borno.
Hare-haren sama da yawa da aka yi da jiragen sama masu saukar ungulu na Alpha-Jets, L-39 da MI-35, sun kashe sanannen Kwamandan ISWAP, Modu Sullum.
Modu Sulum ne ya yi sanadiyyar lalata hasumiyar wutar lantarki a Malanari da ke kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu da kai hari kan matafiya a yankin Auno da Jakana.
Mayakan, a cikin ayarin manyan motoci takwas, sun mamaye Lamboa, a shirye-shiryen kai mummunan hari a yankin Mainok da ke jihar.
Amma cikin hanzari sojojin kasa da na sama suka yi wa ‘yan ta’addanrubdugu inda suka dakile ayyukansu bayan da rundunar ta gano hanyar a baya tun kafin a kai harin ta sama.
An gano cewa da dama daga cikin mayakan ISWAP-Boko Haram sun mutu ta hanyar ruwan bama-bamai na jirgin saman soja.
Lokacin da aka tuntubi Kakakin rundunar sojin saman Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da nasarar da sojojin suka samu a kai.