Rundunar Sojin Saman Najeriya Sun Kaiwa ‘Yan Bindiga Hari A Dajin Doumbourou Dake Jihar Zamfara

Nig-Airforce-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin sama ta gabatar da hari ta jirage a sansanonin yan ta’adda bayan samun rahotanni sirri a dajin Doumbourou yayin da aka gano su suna taro.

Dajin na Doumbourou dake jihar Zamfara da sauran dazuzzuka dake yankin Arewa maso yamma na tattare da manyan bishiyoyi da ruwa da namun dajiwanda ya zama maboyar ta yan ta’addan yankin.

Hakan na cikin rahoton da shugaban rundunar tsaron kasar ya fitar Maj.-Gen. John Enenche wanda yace an gudanar da hare-haren ta sama ranar 13 ga watan Satumba inda yan bindiga da dama suka rasa rayukansu.

San nan yace an tura jirgin yaki da mai saukar ungulu dauke da bama-bama inda suka nufi yan bindigar dake kungiyar Dangote a sabon sansaninsu.

Harin saman shine na farko inda akayi amfani da bam da roket inda aka gudanar a sansanonin yan gudun hijirar na jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto da Neja.

Dandal Kura Radio International ta gana da majiya ta musamman inda ta tambaya kan harin da kuma illar da akayi musu.

Haka nan majiyar tace idan aka lura akwai mata da yara yayin harin ba’a kai hare-haren.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply