Rundunar Sojin Najeriya Ta Cancanci Yabo Ba Wai Kushe Ba Inji MWSN

army
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin Najeriya ta cancanci yabo ne bawai kushe ba injii Dr. Abubakar Mohammed, shugaban kungiyar marubutan sojojin Najeriya.
Dr. Abubakar ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja. Inda yace baiji dadin yadda yan ta’adda da suka hada da yan bindiga suke kai hare-hare a kasar ba.

Haka nan yayi wa wadanda suka rasa iyalansu jaje a hare-haren da aka kai a jihohin Borno da Kastina. Yace duk da tsaiko da aka samu daga jami’an tsaro kan hare-haren da aka kai wasu yankuna na Katsina sun tabbatar cewa jami’an soji na iyakar kokarinsu kuma bai kamata a kushe sub a duk da nasarar da suka samu a watanni 3 da suka wuce.

Haka nan yace lokacin da manyan hafsoshin tsaron suka koma jihar Borno an samu nasarar hallaka yan kungiyar Boko Haram da dama ciki harda kwamandojinsu da masu fita yakin.

San nan ya bayyana rashin jin dadinsu na kalaman mai bada shawara kan sha’anin tsaro na kasa wato Babagana Monguno kan hafsoshin tsaron inda yace a matsayinsa na wanda ya fito daga jihar Borno kuma wanda yasan masu aikata laifukan ya kamata ya dena ganin laifin wasu kamar irin kamfanonin sadarwa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply