Rundunar Sojin Najeriya Sun Fafata Da Yan Kungiyar ISWAP/Boko Haram A Mainok

Rundunar Sojin Najeriya ta samu asarar rayuka bayan harin da ‘yan ta’addan ISWAP / Boko Haram suka kai a garin Mainok da ke jihar Borno.

Har yanzu ba a tabbatar da yawan mutanen da suuka rasa rayukan nasu ba bayan aukuwar lamarin amma rahoton ya ce sojojin Najeriya da ke cikin jiragen yakin Sojan Sama (NAF), a ranar Lahadi sun dakile wani hari na ‘yan ta’addan Boko Haram.

An bayyana cewa ‘yan kungiyar ta ISWAP da’ yan Boko Haram din, sun hau manyan motoci goma sha biyu, sannan suka yi yunkurin tarwatsa wani sansanin sojoji, bayan sun afkawa al’ummar yankin na Minok.

Sun yi yunkurin kwacewa da fatattakar wani sansanin sojoji dake Dogon Karfe a Mainok, amma sun gamu da tirjiya daga sojojin da ke kare yankin inji majiyar rundunar ta NAF.

Sun kara da cewa wasu ‘yan ta’adda sun buya a cikin garin na Minok saboda tsoron hare-hare ta sama.

A cewar majiyar, jiragen NAF ba su harba makami mai linzami a kan maharan ba sun yi dai ta shawagi a sama na awanni don kauce waillata mutanen yankin.

An kuma gano cewa wasu mayakan na ISWAP, da suka ga jiragen yakin, sai suka gudu zuwa makarantar firamare ta Minok don gujewa harin sojojin sama tare da kona ofishin ‘yan sanda saboda fushi.

wadanda suka tsere sun gudu zuwa sansaninsu da ke kusa da lawan Mainari.

A halin yanzu, munanan ayyukan ‘yan ta’adda na zuwa bayan hare-hare da jami’an suka kai a Kumuya, Buni Gari da Geidam a Yobe, haka nan rundunar Sojan Sama ta Najeriya ta girke hanyoyinta na Leken asiri, Kulawa da kuma Sanya ido daga sama