Rundunar Sojin Najeriya Na cigaba Da Yakar Boko Haram

151c3c97-7574-4da3-a9ac-2aa6e2aded4c
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

 

Rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar masu fada aji, na ci-gaba da yakar mayakan Boko Haram sabili da babu wadda ya tsira daga farmakin mayakan.

Mu‘kaddashin mai bada umarni na shiyya ta 7 Birgediya Janar Abdulmalik Biu, shi ne ya bayyana hakan ya yin da sarauniyar maharba Aisha Bakari Gombi, ta ziyarce shi a ofishinsa.

Ya ‘kara da cewa mayakan Boko Haram ba aljanu bane yara ne, ‘ya’ya ne, sa’annan ‘kanne ne don haka watan wata rana za a kau da su.

Haka zalika ya bata tabbacin cewa za su ci-gaba da ya‘kar mayakan don haka akwai bukatar dukkanin wata gudumuwar da ya kamata na ganin an kawo ‘karshen ta’addancin Boko Haram.

A nata 6angaren A’isha Gombi, ta yi wa rundunar sojin godiya da kuma bada na su gudumuwar domin ganin an kawo ‘karshen ta’addancin na Boko Haram na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Har ila yau A’isha Bakari, ta ‘kara da cewa tawagarsu a shirye take ta baiwa rundunar sojin duk wani hadin gwiwar da suke muradi a duk sa’adda a nemu su, kuma kowane lokaci.

Idan za a iya tunawa dai A’isha Bakari, na daya daga cikin dimbin maharan da suka taka rawar gani tare da rundunar sojin Najeriya a sa’ilin da aka fatattaki mayakan Boko Haram, a wasu yankunan da ‘yan ta’addan ke iko da su a yankin Arewacin Najeriya wadda hazakarta ya sanya ake yi mata ‘kirari da sarauniyar maharba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply