Rundunar Sojin Nageriya Ta Mayar Da Martani

Nigerian army thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

 

Rundunar sojin Najeriya ta maida martani game da rubutun da wani marubuci mazaunin ‘kasar Ingila mai suna Dokta Idris Ahmed ya wallafa.

Ahmed Idris ya yi rubutun ne a ranar 23 ga watan Agustan wannan shekarar  mai taken yadda Birgediya Janar Clement Apere ya tura jami’an sojin ke mutuwa a hannun mayakan Boko Haram.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sojin ya sanya wa hannu Birgediya Janar Texas Chukwu, ya ce wannan karya ne, sa’annan ya tabbatar da cewa akwai matakan da hukumomi dake yaki a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ke bi yayin jigbe sojin a fagen daga.

Cikin abubuwan da Dokta Idris Ahmed, ya zargi manyan jami’an sojin ya zayyana cewa suna baiwa mayakan Boko Haram makamai, da yin watsi da jami’an soji 800 da kuma hakala da dama duk zancen kanzon kurege ne.

 

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply