Rundunar soji Ta Tabatar Da Shirin Tura Takai Bango Domin Kawo Karshen Ta’addanci Boko haram da Iswap

DHQ TROOPS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin najeriya ta gabatar da shirin operation TURA TAKAIBANGO domin aiki da gano hanyoyi da suka fi dacewa na yakar yan ta’adda a mabuyar su.

Manjo janar Nuhu Angbazo shugaban bangaren horarsawa na rundunar shi ya bayyana hakan tare da cewa muddin ba’a dauki matakin hakan ba yan ta’adda na iya ci gaba da kaiwa farin hula farmaki a yankunan su kuma su shiga tsakanin mutane musamman a kudanci jihar Borno da Yobe.

Manjo Nuhu ya kuma ce akwai bukatar a dabarun hada yan ta’addan ISWAP dana Boko Haram na yankin arewa mason gabas kasar domin a samo hanya da za’a kawo karshen sace matafiya a babban hanyar Maiduguri-Damaturu wanda shine musabbabin gabatar da shirin na OPERATION KURA TAKAI BANGO.

Major Gen. Angbazo daya wakilce hafsan sojin kasar yayin bayanin ga manema lbaru a makarantar koyan aikin soja na karamar hukumar BuniYadi na jiharYobe.

Yace an kaddamar da shirin “TURA TAKAIBANGO” a ranar 3 ga watan janairun wannan shekara da suka kunshi jihohin Adamawa, Borno, da Yobe na yankin arewa maso gabas.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply