
Shugaban komandar shiyya na 7 na rundunar sojin Najeriya manjo janar Abdul Khalifa ya bada tallafin kayan masarufi ga nakasassu dubu 1 a jihar Borno a cikin kokarin rundunar na bada goyon baya ga masu bukatu a cikin al’ummah.
Abubuwan da aka rabar sun hada da abinci dana sha, taliyar Indomie, kayan sawa da kudi wanda yace zai taimakawa mabukata dake sansanoninn yan gudun hijira da cikin gari tare da cewa ya kasance al’adar rundunar gayyatar mabukata domin tallafa musu a ko wani wata.
A game da batun tsaro, Manjo Khalifa yace hakika alaka tsakanin soji da farin hula ya karfafa tare da cewa an samu nasarar hada kan al’ummah.
Daya daga cikin wadanda sukaci gajiyar tallafin, Abubakar Bulama, ya yabawa komandar shiyyar bisa tallafawa nakasassu. Ya kuma nemi gwamnati da ta kara samar da cibiyoyin koyon sana’o’I a jihar domin basu damar damawa a ayyukan cigaba.
