Rundunar Soji Sun Karyata Rahoto Dake Cewa An Kashe Jami’an Soji 5 A Jihar Borno

DHQ TROOPS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar soji sun karyata wani rahoto dake cewa yan ta’adda sun kashe sojoji biyar kuma suka dauke saura a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu yayin gyarar wutar lantarki ranan litinin.

Mataimakin daraktan jami’I mai hulda da jama’a na rundunar Col. Ado Isa ne ya musanta hakan cikin sanarwa ranan litinin a birnin Maiduguri.

Conel Isa yace rahoton bogi ne kuma bayi da kan gado kuma yaja hankalin jama’a game da rahotannin karya wanda yace anayin sune don undermining yakar ta’addanci.
Hi bub
Sanarwar na kunshe da cewa, sabanin jita-jitar dake yawo, babu wani da aka kaiwa farmaki a ranar na litinin domin babu wani matsala a hanyar duba ma da ziyarar da hafsan sojin kasar ya kawo wa runduna a Ngamdu.

Yace ba’a fara aiki a bangaren wutar na TCN ba domin rundunar daya kamata su baiwa ma’aikatan kariya, sunyi shirye-shiryen karban babban hafsan sojin kasa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply