Rundunar Soji Sun Dakile Wani Hari Da Kungiyar Boko Haram Sukayi Niyyar Kaiwa Karamin Hukumar Gamboru Ngala

DHQ TROOPS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin Najeriya ta dakile wani hari da yan kungiyar Boko Haram suka kai karamin hukumar Gamboru Ngala.

Majiyar rundunar sojin ta shaidawa wakilin mu cewa yan ta’addan sun shiga karamar hukumar ta mashiga da dama wanda rundunar suka fusknace su tare da kashe da dama kuma suka kwato babbar motan bindiga, Babura da sauran makamai.

A cikin ayyukan tsaro da kungiyar taci gaba da yi na yakar yan tada kayar baya, rundunar Operation Tura Ta Kai Bango taci gaba da kutsawa yankunan jihar da dama da nufin zakulo yan ta’addan da suka saura.

Anasa ran rundunar zata dauki sabon salon a yakiar yan ta’addan inda zasu dinga kutsawa mabuyar su tare da fatan kawo karshen su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply