Rundunar operation TURA TA KAI BANGO Na Samun Nasara Akan Yan Kungiyar Boko Haram

FB_IMG_1611786473193
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar shirin operation TURA TA KAI BANGO na yankin arewa maso gabas suna cigaba da tarwatsa yan kungiyar Boko Haram dana ISWAP a mabuyar su a Chindila na jihar Yobe da Mayankari a jihar Borno.

Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan yada labarai na shalkwatan tsaro birgediya janar Benard Onyeuko ya fitar a ranar 26 ga watan nan.

Sanarwar ta bayyana cewa a ranar 25 ga wannan wata da misalin karfe 1 na rana runduna na dari 2 da 33 dake Babbangida yayin wani aikin sintiri sunyi gamo da yan kungiyar Boko Haram a kauyen Chindila.

Rundunar sojojin sun kashe yan ta’addan guda 5 sannan sauran sun tsere da raunin bindiga, kuma sun kwato makamai da suka hada da bindigar AK47 da alburusai.

Rundunar shirin operation TURA TA KAI BANGO suna cigaba da samun nasarori a yaki da suke da yan kungiyar ta’adda wannan na nuni da cewa karshen su yazo a yankin arewa maso gabas.

Haka kuma an yaba da kokarin su na kawar da yan Boko Haram a mabuyar su, kuma an bukace su da su cigaba da kokarin da suke domin samun nasara.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply