
Rundunar shirin operation Fire Ball karkashin shirin Operation Lafiya Dole suna cigaba da nuna kwarewar su da kwazon su wajen yaki day an kungiyar BH da na ISWAP.
Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 7 ga wannan watan ta hannun mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar tsaro birgediya janar Bernard Onyeuko.
Sanrwar ta bayyana cewa a ranar 6 ga watan nan rundunar bataliya na 222 tare da hadin guiwar jami’an sa kai na CJTF sun gudanar da aikin sintiri a yankin kauyen Magumeri.

Haka kuma sanarwar ta kara da cewa rundunar tayi gwabza day an kungiyar BH a yankin, yayi gwambazar tasu rundunar ta kashe yan kungiyar 4 tare da kwato makamai da suka hada da bindiga kirar AK 47 da kirar FN 1 da harhasai da dama da babur guda 2 da kayakin gyaran su da kuma wayan hannu guda 1.
An yaba da kokarin dakarun shirin operation fire ball sakamakon kwazon su wajen yakar yan ta’adda a mabuyar su.
