Rundunar Operation Hadin Kai ta dakile harin Boko Haram a garin Kumshe

Rundunoni na Hadin gwiwa na Operation HADIN KAI (OPHK) da aka tura zuwa Forward Operational Base (FOB) na Bataliyar 152, dake Kumshe a ranar Lahadi, 20 Yuni 2021 sunyi maganin ‘yan ta’addan Boko Haram (BHTs) a kokarinsu na kutsa kai cikin sansanin jami’an.

‘Yan ta’addar sun hau kan manyan bindigogi 4 da babura da dama sun yi yunkurin kutsawa da kuma kai hari sansanin ta hanyar arewacin sansanonin da aka tura sojojin, amma sun gamu da mummunan wuta na sojojin da ke yankin, wanda hakan ya yi sanadiyyar kashe 6 nan take.

Sojojin, sun fatattaki ‘yan ta’addan inda suka tsere cikin rudani baki daya, wanda ya kai ga kame Bindigogi kirar AK 47 guda shida, gurneti, da magunguna daban-daban.

Babban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Faruk Yahaya ya jinjinawa irin matakin da sojojin suka dauka, inda ya bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu tare da tabbatar da cewa an gama da ragowar ‘yan ta’addan da ke aikin sintiri a yankin kwata-kwata.