
Rundunar sojin sama na Operation LAFIYA DOLE ta sake samun nasarra akan yan kungiyar Boko Haram inda suka kashe wasu tare da tarwatsa motocinsu na yaki a kauyen Ajiri a cikin jihar.
Hakkan na kunshe ne a cikin sanarwar da shugaban sashin yada labarai Manjor janar John Enenche ya bayar.
Shugaban ya bayyana cewa an samu nasarar tarwatsasune bayan labara da suka samu n cewar yan ta’adan cikin motocin yaki guda bakwai sun zone da niyar shigowa kauyen Ajiri dake karamar hukmar mafa.

Inda Rundunar suka tura jirgin su mai saukan angulu kuma yayi nassarrar tarwatsa motocin guda biyu kuma ya kashe wasu daga cikin su.
