Rashin Wayar Da Kan Yan Gudun Hijira Na Iya Sasu Kamuwa Da Cutar COVID-19

IDPs
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yan gudun hijira sun fi hatsarin kamuwa da cutar annobar Covid-19 fiye da sauran mutane sakamakon yadda ake cunkusuwa a sansanonin da kuma rashin kayan aikin kiyon lafiya.

Kungiyar lafiya ta duniya ta bada shawarar cewa ya kamata a dinga bada tazara don rage yaduwar cutar ta coronavirus.

Haka nan tace akwai yan gudun hijira da dama da suke zama guri daya cikin rumfuna kuma basu yadda da cutar ba kamar yadda yawancin mutane suke a yankin na Arewa maso gabas.

Wata mata mai suna Aisha Saminu a sansanin yangudun hijira na filin wasa na dake jihar Borno tace tana zama rumfa daya da wasu su 8 amma cikinsu babau wanda ya kama cutar ta Corona.

Haka nan Aisha tace ita bata yadda akwai cutar ba tunda bata taba ganin wanda ya kamu da cutar a inda take ba.

Wan nan rashin yadda da cutar na damun mutane da dama a sansanonin kuma abin damuwa ne.

Haka nan akwai ire-iren Aisha da dama da suke da irin wan nan tunanin tunda basu taba ganin wanda ya kamu da cutar ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply