
Jam’iyar Adawa ta PDP tayi kira ga sabbin shuwaganni sojoji da suyi aiki tukuru domin ganin sun samar da zaman lafiya a cikin kasar.
Jamm’iyar ta kuma bukaci da ayi bincike akan aiki da tsofin sojojin sukayi abaya domin gano asalin abunda yasa ake samun koma baya a harkan tsaro.
A cikin wata sanarwa da sakataren Jam’iyyar Mr Kola Ologbondiyan ya bayar a Abuja ya kirayi sabbin shuwagabannin tsaron da su kara kaimi a daidai wannan lokaci.

Ologbondiyan ya kuma kara da cewa sai sun kara kaini tare da yin aiki kai da fata domin ganin kasar ta koma dadai.
