NSCDC Zata Hada Gwaiwa Da Gwamnatin Jihar Borno Domin Kare Manomar Jihar

NSCDC (1)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar tsaron najeriya da kuma na farin kaya ta nemi hada abokantaka da gwamnatin jihar Borno domin bada tsaro mai inganci ga manoma ta hanyar rundunar tsaron na Agro Rangers da nufin kare sake abkuwar kasha manoma da akayi Zabarmari

A ranar 28th November, 2020 ne dai yan kungiyar BH suka kai farmaki kan manoma a gonaki su inda suka kasha sama dasu 40 a kauyen Koshefe dake jihar Borno
Shugaban rundunar na NSCDC Alhaji Abdullahi Gana Muhammadu ne ya sanar da hakan yayin ziyarar jaje daya kaiwa gwamnan jiha Babagana Zulum a gidan gwamnatin a birnin Maiduguri

Yace suna mika ta’aziyar su ga gwamna da kuma jam’an jihar baki daya bisa kasha-kashen tare kuma da bukatar neman hadin kan gwamnan jiha

inda yace cikin kokarin su na magance matsalar tsaron yankin sun shirya taron bada sanin makamar aiki na kwanaki biyu ya kasance a jihar Borno

Alhaji Zakari Ibrahim Ningi shugaban runduna ne ya wakilce shi inda yace kare raukan jama’a shine gaba domin babu wani cigaba da za’a samu muddin mutane na cikin damuwar tsaro.

ya kuma nuna muhummnaci bada horo ga ma’aikatan ya kuma ce gwamnatin nihar a shirye take da basu goyon baya kuma zata taimaka wajen kare manomn ta rundunar na Agro Rangers

Gwamna Babagana Zulum ya tabbatar wa NSCDC cewa gwamnatin jihar a shirye take ta hada abotan dasu musamman ma day an GH ke komawa yankunan su

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply