Nijeriya: Kungiyar SERAP Ta Aikawa Shuagaba Buhari Wasika Kan Aibanta Shugabanni

20200803_193929
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar bin diddigi ta kasa wato SERAP ta aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika inda ta bukaci da ya bawa miistan sadarwa da al’adu Mr Lai Mohammed da hukumar kula da kafafen sadarwa ta kasa wato NBC umarnin hana kafafen sadarwa umarnin hana batanci ga shugabanni.

Haka nan SERAP ta bukaci shugaba Buhari day a umarci ministan Lai Mohammed da NBC su janye tarar Naira miliyan 5 da aka bawa gidan radiyon Nigeria Info wadda ke kan mita 99.3 zangon FM bayan maganganun da tsohon mataimakin gwamnan babban banki kasar yayi Obadiah Malafia a hirar da yayi a tashar.

A kwanakin nan NBC ta fitar da sanarwa cewa tana gargadin ‘yan jarida da kafafen sadarwa das u daina cin zarafin gwamnoni, ‘yan majlisu, dattijai, da shugabanni wan nan ba al’adar kasar nan bane.

Haka nan sunce hukumar zata dinga saka tara ga duk kafar sadarwar data ki bin wan nan umarnin.
A takardar da SERAF ta mika ga hukumar ta NBC ranar 15 ga watan Augusta na shekarar 2020 wanda mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare yasa hannu yace kungiyarsu ta bukaci NBC da tayi amfani da ofishinta ta ayyukanta ta hanyar samun bayanai, dai-daito da kuma abubuwan da duk suke faruwa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply