
NERI ta samar da littattafai da kujerun makaranta a karamar makarantar Sakandire ta karamar hukumar Geidam dake jihar Yobe kafin a koma makaranta.
Shugaban shirye-shiryen NERI Bukar Kurama yayin bada kayan yace sun bada kayan don karfafa harkar ilimi a yankunann da rikicin ta’addanci ya shafa.
Haka nan yace babban dalilinsu shine a bunkasa harkar ilimi don yara su samu mai inganci.
San nan yace sun bada kayan don taimakawa yankunan da gwamnatin jihar.

Kurama yace sun lura nauyin yayiwa gwamnati yawa yakamata wasu mutane da kungiyoyi su taimaka.
Makarantun da suka amfana sune karammar sakandiren Kawuri, karamar sakandiren maza da mata dake Kafela duk a karamar hukumar Geidam.
