Nigeria: NEMA Ta Raba Kayan Tallafi A Jihar Adamawa

nema 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya ta amince a kaddamar da rabiyar kayan amfani ga YH karkashin maaikatar alamuran jin kai da walwalar jama’a karkashin shugabancin Sadiya Umar Faruk wanda darakta janar na NEMA ze jagoranta a jihar Adamawa.

Shugaban NEMA a Yola Mr. Midala Iliya Anuhu shi ya kaddamar da rabiyar a Fofore. Ya kuma ce rabiyar ci gaban ne cikin ciyar da YH ko wani wata da sukeyi don yaye musu wahalhalu kuma yace a shirye suke suci gaba da hakan.

Yakaru Kachalla, shugaban mata na sansanin yan hijira dake Fufore a madadin sauran yan GH ta godewa gwamnatin tarayya da kuma ministan dama NEMA inda tace sun samu abinci a daidai lokaci da suke bukata tare da cewa sun gode masa kuma suna bukatar taimakon a bangaren lafiya cikin sansanin.

Shugaban gudanarwar a madadin darakta janar in ya bukaci yan gudun hijirar das u kula da matakan kare kamuwa daga COVID 19 sannan ya yi musu fatan ayi bikin babban salla lafiya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply