
Hukumar shirya jarabawa ta kasa ta sake nanata kudurin ta na ganin cewa an gudanar da jarabawa ba tare da wani satar amsaba .
Wannan na zuwa ne a kan zarge-zargen a cikin jarabawar kammala Babban Sakandare ta 2020.
Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a, Azeez Sani, ya bayyana sa hakan a cikin wata sanarwa.

Sani yace majalisar ta samu sanarwar wasu zarge zarge daga cikin zana jarabawar.a makarantar Fabian Kings da makarantar Queens International School, da makarantar Kabala West, dake kaduna .
Ya ce hukumar ta yaba wa mahukuntan gidan talabijin na Sa hannu kan sha’awar da suke da ita wajen tabbatar da tsarkake jarabawar a makarantu tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su yi koyi da wannan aikin.
