Ndume yayi murna tare da taya gwamna Babagana Umara Zulum murnar karramawar digirin digirgir

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sanata mai wakiltar Borno ta kudu Mohammed Ali Ndume yayi murna tare da taya gwamna Babagana Umara Zulum murnar karramawar digirin digirgir a yayin bikin taro karo na 9 na jami’ar Afe Babalola dake Jihar Ekiti.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sanatan ya bayyana jin dadinsa ga jami’ar da ta ba Farfesa Babagana Umara Zulum lambar girmamawa ta digirin girmamawa bisa nasarorin da ya samu a fannin ilimi a matsayinsa na malamin jami’a, mai bincike kuma tsohon shugaban makarantar Ramat Polytechnic Maiduguri.

Sanata Ndume wanda ke cikin tawagar gwamnan a Ado Ekiti, ya bayyana jin dadinsa, inda ya kara da cewa, karramawar ta nuna cewa jami’ar na da cikakken bayani kan irin gudunmawar da ya bayar a fannin ilimi da kuma cigaban al’umma a jihar Borno.

Kamar yadda wani masanin ilimi, dan majalisar ya bayyana, lambar yabon da cewa za ta zaburar da shi wajen cigaba da bayar da gudunmawa wajen gina kasa da kuma al’umma baki daya.

Sanarwar ta kuma yi masa fatan alheri yayin da ya cigaba da kokarin neman cigaban jihar da kuma yantar da talaka.
PRR/BBW

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply