NDLEA Ta Kwace Kwayoyi Kilogram 17,000 A Jihar Borno

ndlea large
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi na najeriya NDLEA a jihar Borno ta kwace miyagunn kwayoyi da yakai kilogram 17,000 dubu tare da capke masu ta’amuli da miyagun kwayoyin guda 544 tun janairu zuwa disamban shekarar 2020 daya gabata.

Komandan hukumar Mr. Joseph Icha ne ya bayyana hakan yayin jero irin nasarori da hukumar ta samu a shekarar.

Mr Icha ya bayyana cewa cikin mutane 544 da aka capken, akwai maza 537 mata kuma guda 7. Ya kuma ce hukumar ta kuma kwato motoci guda goma tare da cewa tuni an samu bayanin 3 daga ciki.

Komandan yace abin al’ajabi shine yadda aka yawan amfani da miyagun kwayoyin a sansanonin yan gudun hijira wanda yace hukumar tafara amfani da fasaha domin binciko yadda al’amuran suke a sansaonin.

Wakilin mu ya ruwaito cewa, a watan agustan bara, hukumar ta lalata miyagun kwayoyi da nauyin su yakai kilogram dubu 19,234.58 da suka hada da hodar iblis, kwayar tramadol, wiwi da sauran su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply