NCC Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Tallan Bayar Da Katinan Karya Daga Davido

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta sanar da ‘yan Najeriya game da wani tallan karya da aka ce Davido ya yi a kafafen sada zumunta.

Dr Ikechukwu Adinde, Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar NCC, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata a Abuja, ya ce wasu gungun ‘yan damfara sun kaddamar da wani talla mai taken “Davido Airtime and Data giveaway.

Ya ce tallar na cigaba da yaduwa, ta inda akayi ikirarin cewa Davido yana bayar da kyautar N5,000 na kati da kuma bayanan intanet na 10GB a dukkan hanyoyin sadarwa domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Ya ce hukumar ta NCC ta gano a yayin da take gudanar da sauraren ra’ayoyin jama’a ta yanar gizo, cewa wata kungiya ce da ba a san ta ba, take shirin damfarar jama’a da ba su ji ba gani.

Adinde ya ce miliyoyin masu amfani da wayar tarho a Najeriya abin ya shafa, saboda masu damfarar sun yi amfani da karimcin David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido.

Tauraron mawakin nan Ba’amurke kuma dan Najeriya, marubuci kuma furodusa kwanan nan ya bayyana cewa zai bayar da gudunmuwar Naira miliyan 250 ga gidajen marayu daban-daban a fadin Najeriya.

Don haka Hukumar NCC ta nanata gargadin da ta yi tun farko ga masu amfani da wayar da su yi taka-tsan-tsan, kar su fada ciki don ba gaskiya bane.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply