NANS Tayi Barazanar Kulle Makarantu Jami’a Masu Zaman Kansu

schools
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar dalibai na kasa (NANS) tayi barazanar rufe makarantun jami’a mai zaman kansu a fadin najeriya har sai ASUU ta dawo daga yajin aiki wata 9 wanda aka farashi tun watan maris na wannan shekara a dalilin rashin biyan su alawus da kuma tsarin biyan albashi na IPPIS wanda malaman sukaki amincewa da hakan.

Shugaban kungiyar Asefon ya koka da cewa yajin aikin shine mafi tsawo da malaman jami’an suka taba yi kuma yace zasu zauna da wakilan gwamnatin tarayya da kuma shuwagabannin ASUU don samar da mafita tsakanin bangarorin
Yace idan ba’a samu mafita ba to babu abinda ya rage face rufe dukkan manyan makarantun a kasar.

Biyo bayan gyarn fuska da gwamnatin tarayyar tayi na kara kudi daga naira biliyan 65 zuwa naira biliyan 70 domin biyar sauran alawus dama gyaran jami’o’in, shuwagabannin na ASUU sun amince da hakan saide sun dage cewa dole a fara biyan kudaden da aka iken kuma bata hanyar tsarin biyan na IPPIS ba kafin su janye yajin aikin.

A baya an saka ranar 9 ga watan decemba na wannan shekaran domin gwamnatin tarayya ta gana da shuwagabannin ASUU sai de kuma ASUU ta nemi a dage zaman da cewa lokacin da aka deben ya mata kadan da har zata gana da mambobin ta.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply