Najjeriya: Gwamnonin Arewa Zasu Hada Kai Da Yan Sakai Don Dakile Matsalar Tsaro

NGF
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnonin Arewa Sun Dauki Sabon Mataki inda Suka Kafa Kwamiti Da Zai Dauki Matakin Kula Da Yan Sa Kai, Mafarauta, Da Kungiyoyin Al’umma Kan Matakin Leken Asiri Da CiGaba Da Sanya Ido A Yankin.

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, Ne Ya Bayyana Hakan A Wata Sanarwa ta bakin Mai Magana Da Yawun Sa Makut Macham Ya Fitar Ranar Juma’a A Garin Jos. Yace Aikin Wani Bangare Ne Na Kudirin Gwamnonin Arewa Na Kawo Karshen Tadanci A Kasar.

Lalong, Ya Ce Kwamitin Zai Kuma Yi Shawarwari Tare Da Shugabannin Gargajiya, Da Na Addini Da Kuma Shugabannin Al’umma A Arewa, Don Karfafa Rawar Da Suke Takawa Wajen Shawo Kan Matsalolin Tsaroa Kasar .

Kwamitin Da Ke Kan Tsaro, Wanda Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Ya Jagoranta, An Kuma Kafa Ta Don Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Hukumomin Tsaro Wajen Aiwatar Da Matakan Tsaro A Yankin.

Taron Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Sa Ido Sosai Kan Kungiyar Ecowas Ta Kan Iyakokin Makiyaya Daga Wasu Kasashe Zuwa Cikin Najeriya.
Yayin Taron Sun Baiyana Taaziyansu Ga Jihohin Da Akai Musu Hari Da Sauran Nau’o’in Taadancin A Yankin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply