Najeriya Zata Fara Fitar Da Mai Nan Da Shekarar 2023 – Kyari

mele kyari k
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban hukumar man fetur ta kasa wato NNPC, Mele Kyari yace yadda Najeriya take samar da mai a a kowace rana a yanzu yafi yarjejeniyar da suka kulla a tsakanin manyan kasasshe masu samar da man.

Shugaban na NNPC ya bayyana hakan yayin taron da Atlantic Council ta shirya inda yace idan dukkanin kasashen dake karkashin OPEC zasu yarda yarjejeniyar baza ta kai watan Augusta ba.

Kyari yace Najeriya, wadda na daya daga cikin manyan kasashen da suke fitar da mai, kuma hukumar ta na aiki kan tabbatar da cewa Najeriya ta dena shigo da man nan da shekaru uku.

Haka nan yace gwamnati na kokarin yanke shawarar kafa wata matatar man da zata dinga sarrafa Karin samar da man nan da watan Yuli.

Wanda zai samar da gangar mai 50,000 a kowace rana kuma suna shirin gyara matatan man dake kasar baki daya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply