Najeriya: Za’a Fara Jarrabawa WAEC Daga 4 Ga Watan Augusta Zuwa 5 Ga Watan Satumba

WAEC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An tsayar da watan Augusta a matsayin lokacin da za’a gudanar da jarrabawar WAEC.

Karamin Ministan ilimi Emeka Nwajiuba ne ya bayyana hakan ranar litinin yayin bada jawabi ga kwamitin yaki da cutar COVID-19 a Abuja.

Yace daga wancan satin shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 ya bayana cewa za’a samar da kayan aiki ga wadanda zasu fara darussa kan abubuwan da aka koya.

Haka nan yace jihohin da suke da niyya zasu iya fara darussan, san nan yace ranakun da aka saka na fara jarrabawa shine daga 4 ga watan Augusta zuwa 5 ga watan Satumba.

Ya kuma kara da cewa hukumar zata wallafa lokutan jarrabawar bayan taron da zasu gudanar da cibiyar yaki da cututtuka ta kasa, kungiyar malamai ta kasa da kuma masu ruwa da tsaki.

Nwajiuba ya kuma bayyana cewa in an gama jarrabawar WAEC gwamnati zata fara shirin NECO da kuma jarrabawar NABUTEX

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply