Najeriya: Za’a Fara Gudanar Da Karatu A Jami’ar Jihar Borno

kashim
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya Kashim Shettima yace zai bayyana masu kula da jami’ar jihar wan nan watan don a fara gudanar da karatu a wan nan shekarar.

Gwamnan ya bayyana hakan yayin da ya gana da manema labarai a Maiduguri inda yace an samu rashin fara karatun da wuri sakamakon ganin an inganta jami’ar da kayan za’a iya kwatantasu da jami’oin zamani mai zuwa a fadin kasar.

Ya kara da cewa duk aikin gidajen da akeyi a cikin birnin Maiduguri da kana nan hukumomi za’a karasa su kuma za’a rabawa wadanda suka dace nan da wata 3.

Kashim Shettima ya danganta rashin gama aikin da wuri da cikas din tsaro da ake samu amma yanzu an samu tsaro inda wasu yan gudun hijira na a guraren.

Ya kuma bayyana takaicin sa na yadda rikicin ta’addanci yayi sanadiyyar lalata gurare da dama kamar makarantu, asibitoci, amma ya dau alwashin ganin sun gyara guraren don aci gaba da amfani dasu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply