Najeriya: Yansanda Na Farautar Wadanda Suka Kashe Dalibar Jami’ar Benin

STUDENT
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar yansandan jihar Edo na nan na farautar mutanen da suka yi sanadiyyar kisan dalibar jami’ar in Benin a jihar Edo.

Dalibar mai suna Vera Omozuwa yar ajin farko a Microbiology, an mata duka a dakintaro na cocin Redeemed Christian dake Ikpoba Hill a birnin Benin City ranar 13 ga watan Mayu yayin da taje karatu.

Dalibar yar shekaru 23 ta rasu ranar 31 ga watan Mayu, kwana 18 bayan an kwantar da ita a asibitin jami’ar ta Benin.

Mai Magana da yawun yansandan jihar Chidi Nwabuzor yace ranar da abun ya faru bata cikin hayyacinta shi yasa basu samu daukan rahoto ba daga bakinta.

Mr Nwabuzor yace yansandan yankin sun gana masu kula da coin inda duk suka musanta cewa basa gun da abun ya faru don haka baza su iya tabbatarwa cewa an mata fyade ba har sai sun samu sakamakon asibiti.

Haka nan gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya bawa yansandan jihar umarnin zakulo wadanda suka kasha Omozuwa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply