
Shugaban rundunar sojin Najeriya Leuternant t Gen Yusuf Buratai ya bayyana cewa yan ta’adda sun juyarda ayyukansu zuwa yankin Arewa maso tsakiya.
Ya bayyana hakan ne yayin bikin bude sashin sojoji dake Barikin sojoji a garin Doma dake jihar Nasarawa.
Buratai, ya bayyana hakan tab akin mai kula da tsare-tsare na rundunar Lt Gen Lamidi Adeosun, inda yace yadda ake samun kalubale a kasar akwai bukatar jami’ai kwararru masu dabarar aiki da zasuyi aiki a kowane irin yanayi.
Haka nan yace zasu zauna dundin-din a Doma amma zasu dinga ayyukansu ga kasar baki daya. San nan yace tunda ya kama aiki a matsayin shugaban rundunar kullum yana ganin sojojin na karuwa amma hakan baya sa a dena samun kalu bale a kasar.
Yayin da yake Magana lokacin assasa ginin a hedikwatar rundunar dake Doma, Gwamna Abdullahi Sule of Nasarawa ya yabawa shugaban rundunar sojin kan dagewa da kokarin da yakeyi na yaki da ‘yan ta’adda a arewa maso gabas, da rikicin manoma da makiyaya da kuma na yan bindiga daga yankin Arewa maso yamma.
