Najeriya: Yan Majalisar Jihar Bauchi Sunyi Kira Da A Magance Matsalar zaizayar Kasa

map-of-bauchi-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Fatima Idris Danjuma, Bauchi

Majalisar jihar Bauchi tayi kira ga gwamnatin jihar data magance matsalar zaizayar kasa da ake fama da ita a wasu daga cikin kanannan hukumomin jihar.

Alhaji Dan’umma Bello mai wakiltar ryankin Giade ne ya mika wan nan kudurin yayin zaman majalisar ranar Talata a Bauchi.

Yan majalisar sunce zaizayar kasar na shafar yankunan jihar a karamar hukumar Giade kuma akwai bukatar gwamnatin jihar ta ceto yankin.

Acewar sa gwamnatocin da suka wuce sun bada ayyukan gina titin daga Giade zuwa Jugudu zuwa Kurba amma saboda matsalar tattalin arziki da kuma annobar covid-19 ba’a gudanar ba. Haka nan yace zaizayar tana wanke wani gefen a kan titin garin Jugudu.

Bello ya kara da cewa a yanzu zai-zayar naso da ci titin Azare zuwa Misau da kuma kauyukan shinkani, Sabon Sara, Isawa, Kurba, Zirami.

San nan yayi kira gay an majalisar dasuyi kiraga majalisar data kafa kwamitin da zai gano abinda ke faruwa don daukar mataki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply