Najeriya: Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kashe Sojoji 9, Sun Jiwa 2 Rauni

bh small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Boko Haram sun kashe sojoji tara sun jiwa mutum biyu ciwo a Arewa maso gabashin Najeriya.

Ana ci gaba da samun wan nan hare haren bayan ance Sojoji sun kakkabe dajin Sambisa, sannan gwamnatin na ikirarin an ci karfin yan Boko haram din suna guduwa, haka nan ana kiran yan gudun hijira su koma garuruwansu yankin.

Jami’an runduna ta bataliya 242 na rundunar sojojin Najeriya dake Gajiram a arewacin Borno sun gamu da hari ranar litinin da rana.

Yansandan jihar ta Borno sun bayyana cewa sojojin sun dakile harin a take bayan an kai musu kuma ba’a samu rauni ba. Amma rahoton da sojojin suka fitar ta AFP sunce sojoji 9 sun rasu 2 kuma sun samu rauni.

Mazauna yankin sun bayyana cewa sunga an saka yan Boko Haram 10 zuwa 12 a mota basu san nawa ne suka rasu ba ko nawa suka ji ciwo. Har yau dai ba’a samu bayani daga bakin mai Magana da yawun rundunar ba wato Brigadier General Texas Chukwu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply