Najeriya: ‘Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kai Hari Magumeri Dake Jihar Borno

A screengrab taken on November 9, 2014 from a new Boko Haram video released by the Nigerian Islamist extremist group Boko Haram and obtained by AFP shows Boko Haram fighters parading on a tank in an unidentified town. The leader of the Nigerian Islamist extremist group Boko Haram, Abubakar Shekau, dismissed again government claims about ceasefire talks and threatened to kill the man who has presented himself as Boko HaramТs negotiator.  AFP PHOTO / HO / BOKO HARAM

= RESTRICTED TO EDITORIAL USE - MANDATORY CREDIT

A screengrab taken on November 9, 2014 from a new Boko Haram video released by the Nigerian Islamist extremist group Boko Haram and obtained by AFP shows Boko Haram fighters parading on a tank in an unidentified town. The leader of the Nigerian Islamist extremist group Boko Haram, Abubakar Shekau, dismissed again government claims about ceasefire talks and threatened to kill the man who has presented himself as Boko HaramТs negotiator. AFP PHOTO / HO / BOKO HARAM = RESTRICTED TO EDITORIAL USE - MANDATORY CREDIT "AFP PHOTO / BOKO HARAM" - NO MARKETING NO ADVERTISING CAMPAIGNS - DISTRIBUTED AS A SERVICE TO CLIENTS =

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

yan kungiyar Boko Haram terrorists sun kai hari karamar hukumar Magumeri dake jihar Borno ranar Litinin inda suka kona Wayoyin kafafen sadarwa na wayar tafi da gidanka da sauran ababben more rayuwa.

A satin da ya gabata ma yan kungiyar sun kai hari garin na Magumeri da kewaye inda manoma da makiyaya da dama suka gudu bayan sun kashe mutum 6 wasu sun samu raunuka.

Magumeri na arewacin jihar Borno da nisan kilomita 40 daga birnin Maiduguri babban birnin jihar wanda yasha fuskantar hare-haren yan kungiyar ta Boko Haram ciki harda garkuwa da masu hakar mai da suka je daga jami’ar Maiduguri a yankin tafkin Chadi.

Wanda ya hada mana rahoton ya bayyana cewa yan kungiyar sun mamaye yankin da misalin karfe 4 na yamma inda jami’an sojin sama suka bude musu wuta amma sai da suka samu suka shiga garin wanda yasa sojin suka sassauta saboda sun shiga cikin al’umma.

Dan majalisar dake wakiltar Magumeri, Gubio da Kaga a gwamnatin tarayya Hon Usman Zannah ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply