
Wasu da ake zargi yan bindiga sun kashe dan majalisar tarayya na jihar Bauchi mai wakiltar shiyyar Baraza/Dass Alhaji Musa Mante.
Majiyar ta bukaci da a sakaya sunanta yayin da takeyiwa manema labarai jawabi a Bauchi inda tace an kasha Mante a daren Alhamis a gidansa dake Dass.
Haka nan tace yan bindigar da ake zargin yan fashi da makami ne sun zagaye gidan marigayin suka harbe shi cikin daren.

Mai Magana da yawun yansanda da hulda da jama’a na yankin DSP Ahmed Wakil ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace yan bindigar sun yi garkuwa da matan dan majalisar 2 da yaronsa namiji.
Haka nan ya tabbatar da cewa zai bayyanawa manema labarai wajabin idan sun gama bincike.
