Nigeria ta shirya tsaf don kawo wasu sabbin jiragen yaki guda 3 samfurin JF-17 Thunder, yayin da kasar ke ci gaba da karfafa amfani da sararin samaniya domin ayyukan tsaro na cikin gida.
Jirgin zaiyi amfani a kowane yanayi, dare da rana , jirgin yakin na daya daga cikin jirage na zamani inda za’a kaddamar dashi a ɓangaren rundunar Sojan Sama na Najeriya inda za’a ajiye jirgin Anglo-Faransa SEPECAT Jaguar jets wanda ake amfani dashi tun a farkon 1990s.
Jirgin yakin JF-17 masana’antar hadin gwiwa ce ta kamfanin Chengdu Aircraft Industry Corporation na China da Pakistan Aeronautical Complex na Pakistan ne suka kera shi.
A cewar Rundunar Sojin sama, baje kolin jirgin zai zo a ranar cikar rundunar shekaru 57 da aka shirya gudanarwa tsakanin 19 zuwa 20 ga Mayu a tsakiyar Arewa ta tsakiyar garin Makurdi, Jihar Benuwai, inda Tactical Air Command (TAC) yake.
A watan Disamba na 2020, an ga jiragen sama uku na NAF JF-17 a lokacin da aka gabatar dasu.
Dandal Kura Radio International ta fahimci cewa matsalolin fasaha, na’ura da na aiki da ke tattare da karamin jirgin da aka samu kuma na iya yin tasiri ga samuwar jirgin don ayyukan soji a kan kungiyoyin masu dauke da makamai.
Har yanzu ba a bayyana lokacin da sojojin sama za su yi umarni na gaba ga JF-17 da kuma wane irin jirgi za a saya.
Sojojin saman suna kuma jiran isowar jirgi 12 A-29 Super Tucano daga Amurka, tare da rukunin farko na jirgin da ake sa ran zai sauka a Kainji Airbase a karshen zango na Biyu na 2021.