Najeriya Ta Kara Samun Mutane 745 Masu Dauke Da Cutar COVID19

NCDC 3
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Najeriya ta kara samun mutane 745 masu dauke da cutar COVID19 a kasar inji cibiyar yaki da cututtuka ta kasa wato NCDC.

DANDAL KURA RADIO INTERNATIONAL ta gano cewa wan nan ne karon farko da aka samu mutane masu yawan gaske tunda aka fara annobar a kasar a watan fabarairu.

A yanzu ana da mutane 18,480 a kasar bayan da aka gwada mutane 106,006. Jihar Lagos ce kan gaba a yawan mutanen da mutane 280, sai jihar Oyo da mutane 103, sai Ebonyi mai 72, FCT had 60, Imo 46, Edo 34, Delta 33 and Rivers 25.

Sai jihohin Kaduna 23, Ondo16, Katsina 12, Kano 10, Bauchi 8, Borno 7, Kwara 5, Gombe 4, Sokoto 2, Enugu 2, Yobe 1, Osun 1 da Nasarawa 1.

DANDAL KURA RADIO INTERNATIONAL ta rawaito cewa an sallami mutane 6,307 sai 475 da suka rasa rayukansu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply