Najeriya ta kaddamar da shirin “Project Zero Hunger” ga yan gudun hijira.

Hukumar kula da yan gudun hijira tare da hadin guiwar kungiyar matan jami’an tsaro da na yan sanda sun kaddamar da shirin “Project Zero Hunger” da nufin tallafawa yan gudun hijira da sauran kungiyoyin marasa karfi a jihohin dake fadin kasar nan.

Da take magana a wajen taron a sansanin yan gudun hijira na Durumi a Abuja, ministar harkokin jin kai da walwalar jama’a Sadiya Umar Farouq, wanda ta samu wakilcon daraktan al’amuran jin kai Grema Ali tace aikin zai baiwa masu ruwa da tsaki damar ciyar da mutum daya tare da hadin kai mai dorewa za’a kawar da yunwa.

Tace tare da daukaka nayi maraba da ku gaba daya zuwa wannan lokaci domin kaddamar da shirin PROJECT ZERO HUNGER a karkashin kulawar hukumar kula da yan gudun hijira ta kasa.

Ma’aikatar harkokin bada agaji da walwalar jama’a karkashin jagorancin shugaba Buhari kwanan nan ta sanya hannu kan manufar yan gudun hijira a Najeriya.