Najeriya: Sojoji.Sun Dakile Harin Da Aka Kai Garin Kukawa A Jihar Borno

THE TROOPS OF OPERATION LAFIYA DOLE
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar soji karkashin operation Lafiya Dole sun ceto garin Kukawa mai dogon tarihi wanda ke Arewa maso gabashin Najeriya daga harin da yan kungiyar ISIS suka kai garin

garin na Kukawa na kusa da gabar Tafkin Chadi wanda yan kungiyar suka kai masa harin.

A rahoton da Major General John Eenenche, mai kula da tsare-tsare na rundunar ta fannin yada labarai yace sojojin dake yankin sun dakile harin.

Enenche yace yayin fafatawar sun kashe yan kungiyar 8 da kuma da dama da suka gudu da raunuka.

Haka nan yace idan za’a iya tunawa ranar 29 ga watan Juli na shekarar 2020 gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da sakebude tirin Munguno zuwa Cross Kauwa.zuwa Kukawa.

san nan yace yan kungiyar sun kai harin don maida hannun agogo baya a kokarin da gwamnan yake na maida yan gudun hijira da sake gine-gine.

A shekaruda dama rikicin na Boko Haram yayi sanadiyar rasuwar mutane kimanin 30,000 da kimanin mutane milyan 3 da suka rasa mtsugunan su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply