Najeriya: Sojoji Basu Samu Kudadensu Ba Na Shekarar 2020 – Ndume

Ali-Ndume-600x450
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kwamitin sanatoci kan Jami’an soji Sanata Ali Ndume yace Sojoji basu samu kudaden day a kamata ba duk da kokarin da kasar takeyi na yaki da yan ta’adda da yan bindiga.

Yace babu kudin da aka basu na kudaden day a kamata na shekarar 2020 wanda gashi ana watan Juni a yanzu. Haka nan yace shugaban kasa ya bada umarnin dakile sha’anin tsaro a kasar amma mutanen day a kamata su bada kudaden sojojin basa yin yadda ya kamata.

Ndume ya kara da cewa shugaban rundunar sojin kasan Tukur Buratai ya koma cibiyar da ake aikata ayyukan ta’addanci a kasar don ya karfafawa jami’an dake yakin karfin gwiwa mazansu da matansu.

Haka nan yace komawar Buratai yankin ya sa an samu canji don haka jami’an na bukatar abubuwan da zasu taimaka musu.
Ndume yace idan za’a iya tunawa Boko Haram sun kasha fiye da mutane 50,000 a Arewa maso gabas da kuma tsugunar da miliyoyin mutane dayin garkuwa da wasu tunda suka fara yaki a shekarar 2009.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply