Najeriya: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Kan Yaki Da Ta’addanci

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi taimakon sarakunan gargajiya wajen yaki day an ta’adda a kasar.

Shugaban yayi kiran a fadar sarkin musulmi na Sokoto Muhammad Sa’ad Abubakar inda yace sarakunan gargajiyar sun taka rawa ta musamman wajen samar da zaman lafiya a kasar.

Babban akanta na kasa kuma Ministan shari’a Abubakar Malami ne ya wakilci shugaban kasar inda ya jagoranci ministan kula da harkar yansanda Muhammad Maigari Dingyadi, shugaban yansandan kasar Muhammad Adamu wajen daurin auren yayan marigayi Ambassador Shehu Malami da marigayi Alhaji Musa Abubakar.

Malami yace gwamnatin bata gajiya ba wajen yaki da yan ta’adda day an bindiga a kasar da ragowar ayyukan ta’addanci.

Haka nan yace shugaba Buhari ya bukaci dasu mika godiya ga sarkin musulmin kan taimakon da yake bayarwa gwamnatinsu musamman kan sha’anin tsaroe day a addabi kasar.

A nashi bangaren sarkin musulmin ya bayyana cewa zasu cigaba da iyakar kokarinsu har sai abubuwa sun dai-daita a najeriya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply