Najeriya: Shugaba Buhari Yace Hafsoshin Tsaro Basa Daukar matakan Da Ya Dace

chiefs
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa kan ayyukan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a sassan kasar nan inda yace hafsoshin tsaron basa daukar matakan da suka dace.

Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Maj.-Gen. Babagana Monguno ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasar bayan ganawar sirri da yayi da shugaban kasar dake Abuja.

Monguno yace shugaban ya nuna bacin ransa kan rashin hadin kai da ake samu cikin jami’an tsaro wajen yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.

Haka nan yace shugaban kasar yace bazai yadda da karuwar ayyukan ta’addanci a kasar ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply