Najeriya: Shugaba Buhari Ya Dakatar Da Sakataren Hukumar EFCC

EFCC 4
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Manyan ma’aikatan hukumar EFCC su 11 bayan da binciken da akewa tsohon shugaban hukumar Ibrahim Magu ya zurfafa.

Sakataren hukumar ta EFCC Olanipekun Olukoyede na daya daga cikin wadanda shugaban kasar ya dakatar. Olukoyede ya zama sakataren hukumar a watan Nuwamba na shekarar 2018bayan da yan majalisar dattijai suka tantance shi.
Acewar majiyar tamu an sdakatar dasu ne sakamakon zarge – zarge da ake dasu akansu da cin hanci da kuma samun damar ayi bincike.

Haka nan rahoton yace an dakatar da dukkanin manyan hukumar kuma duk an kulle ofisoshinsu an tsoron a nemi wasu takardun fayil din dake hukumar a rasa.

Shugaba Buhariya dakatar da tsohon shugaban hukumar Ibrahim Magu a satin daya wuce inda ya nada Daraktan kula da hukumar Mohammed Umar Abba.

San nan majiyar tace Umar Abba ya samu mukamin ne bayan tabbatarwa da akayi baya da hannu a cikin abubuwan da ake binciken.

Tsohon shugaban hukumar naci gaba da samu matsin lambakan binciken da ake masa karkashin kwamitin da shugaban kasa ya kafa wanda mai shari’a Ayo Salami yake jagoranta kan zarge-zargen kudade.

Haka nan a nan ana cigaba da bincikenshi kan kudaden da aka kwato ana zargin ya kwashe.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply