Najeriya: Shugaba Buhari Ya Bukaci Da A Samar Da Zamnan Lafiya A Yankin Arewa Maso Gabas

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana tashin hankalin da yan kungiyar Boko Haram suke haddasawa shekaru 10 a arewa maso gabas a matsayin babban abun tashin hankali, donhaka akwai bukatar bada himma wajen farfado da yankunan da abun ya shafa da sake ginasu, da samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin baki daya.

Ministar jin dadi da walwalar jama’a Hajiya Safiya Umar Farouk ce ta wakilci shugaban yayin bikin mika motocin jami’an tsaro 120 ga rundunar sojin Najeriya da kuma motocin daukar marasa lafiya a yankin.

Yace farfado da yankin da samar zaman lafiya ne abubuwan da yake da bukata tun da aka rantsar dashi a matsayin shugaban kasa.
Haka nan yace dole a hada hannu da karfe da masu ruwa da tsaki don farfado da harkar tsaron wanda majalisar dinkin duniya ta kiyasta za’a kasha dala biliyan 9.2.

Shugaban sanatocin Najeriya Senator Ahmed Ibrahim Lawan ya roki hukumar NEDC data hada kai da gwamnatin jihar Borno don sake gina yankin da kayayyakin more rayuwa kamr titinan da suka lallace

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply