Najeriya: Shugaba Buhari Ya Amince Da Saka Sunan Goodluck Jonathan A Tashar Jirgin Kasa Ta Agbor

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan sufuri Rotimi Amaechi yace sun sirya tsaf don kaddamar da hanyar jirgin kasa data fara daga Warri-Itakpe.

Ya bayyana hakan ne yayin da kai ziyarar aiki wajen inda ya bayyana farin cikinsa na yadda ayyukan da suke gudana.

Acewar sa an gama tashoshin jirgin kasan guda 10 kuma shuagaban kasa Muhammadu Buhari ya amice da saka sunan tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan a babbar tashar ta Agbor.

San nan ya kara da cewa tashar jirgin kasar zata fara ayyukan diban kaya daga tashar jirgin ruwa dake Warri, haka nan duk wani abu da aka sarrafa daga Ajaokuta za’a kaishi a jirgin kasa.

Amaechi yace sun fara tattaunawa da Dangote da BUA kan daukar siminti a jirgin kasan na daukar kaya yana fara aiki.

Haka nan yace a yanzu bazai iya bada lokacin da za’a fara ba saboda aikin yayi baya sakamakon annobar Coronavirus.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply